WHO ta sauya ka'idoji kan masu HIV

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption An sauya ka'idojin shan maganin HIV

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sauya ka'idojinta a kan masu dauke da kwayar cutar HIV, tana cewa daga yanzu duk wanda aka same shi da kwayar cutar dole ne a bashi magani nan take.

WHO ta ce gwaje-gwajen lafiya sun nuna cewa fara shan maganin da wuri yana taimakawa wajen tsawaita rayuwar masu dauke da kwayar cutar tare kuma da rage yaduwar kwayar cutar, wadda take jawo cuta mai karya garkuwar jiki.

A can baya dai hukumar ta shawarci Likitoci da kada su bai wa masu dauke da kwayar cutar magani har sai garkuwar jikinsu ta fara nuna alamun rashin lafiya.

A yanzu mutane da yawa a duniya daga miliyan 28 zuwa miliyan 37 za su ci gajiyar shirin bayar da maganin rage karfin cutar sakamakon sabbin ka'idojin da aka fitar.

Kungiyar Likitocin duniya ta MSF, ta ce ana bukatar kara samun goyon baya daga gwamnatoci da masu bayar da tallafi domin ganin an cimma wadannan sabbin ka'idoji.