2019: Dan takarar PDP zai fito daga arewa

Image caption Jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin don nazarin yadda za ta bullowa al'amuranta.

A Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta PDP na duba yiwuwar tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 daga arewacin Najeriya.

Kwamitin da jam'iyyar ta kaddamar domin nazari kan dalilan da ya sa jamiyyar ta sha kaye a babban zaben kasar na wannan shekarar ne ya bada shawarar hakan a rahotansa daya mika.

Kwamitin ya ce tun da dai a zaben shekara ta 2015, mutumin da ya tsaya wa jam'iyyar takarar shugaban kasa ya fito daga kudanci, to zai fi dacewa in wani daga arewaci ya tsaya a shekara ta 2019.

A watan Mayu ne jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin don nazarin yadda za ta bullowa al'amuranta, tun bayan babban zabe na shekara ta 2015.