Mota mai kofofi kamar fuka-fukai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Farashin motar kirar Model X ya fara ne daga dala dubu $144,000

Kamfanin Tesla da ke kera motoci masu amfani da wutar lantarki ya kaddamar da mota kirar Model X da aka dade ana tsammani da ke da na'urorin kariya tare kuma da kofofi da ake bude wa sama kamar fuka-fukai.

Wannan ne karo na uku da kamfanin ke kera motoci kuma an kaddamar da motocin ne shekaru biyu kafin lokacin da aka shirya kaddamar da su tun da farko.

Duk da cewa kamfanin bai sanar da ribar da ya samu ba cikin shekara guda, amma ya ce kimanin mutane dubu 25,000 suka riga suka yi odar sabuwar motar da aka fitar.

Farashin motar kirar Model X ya fara ne daga dala dubu $144,000 kuma kamfanin Tesla na fatan gabatar wa mutanen da suka yi odar motar cikin watanni takwas zuwa shekara guda.