An kama Janar Diendere a Burkina Faso

Image caption Janar Diendere ya mika wuya

An mika jagoran juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso a watan jiya, Janar Gilbert Diendere, ga hukumomin kasar.

Tun da farko dai gwamnatin ta ce ana tattaunawa a wani ofisihin jakadanci da ba a bayyana shi ba a babban birnin kasar Ouagadougou a kan yadda janar din zai mika wuya.

An ba da rahoton cewa Janar Diendere ya samu mafaka ne a ofishin jakadancin Fadar Paparoma ta Vatican.

Ranar Talata ne dai sojojin kasar suka bude wuta a kan wani bariki inda magoya bayansa wandanda suka ki ajiye makamansu daga cikin rundunar tsaron shugaban kasa suke.

Shugaban rikon kwarya na kasar Michel Kafando ya yaba wa sojojin "Daga yanzu, sojojinmu sun maido da martabarsu. Muna girmama sojojin kasarmu wadanda suka cimma wannan gagarumar nasara ta kawo karshen tawaye ba tare da zubar da jini ba."