Mahajjatan Iran 464 ne suka rasu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Hassan Rawhani na Iran

Iran ta ce yawan 'yan kasarta mahajjata wadanda suka rasu a turmutsutsun da aka yi a Saudiyya a makon da ya gabata, ya kai 464, adadin ya nunka abin da aka fada a baya.

Hukumomi a Iran din sun ce sun fitar da rai na ganin wasu mahajjatan kasar da ransu.

A cewar Jami'an Saudiyya mutane 769 ne suka mutu a turmutsutun a Mina da ke kusa da Makkah kuma wasu 934 suka jikkata.

An soki Saudiyya a kan matakan tsaro da kuma jinkiri na wallafa sunayen wadanda abin ya shafa.

Jami'an Iran din sun yi zargin cewa yawan mutanen da suka mutu a yanzu sun fi 1,000.

Kasashen Pakistan da India da kuma Indonesia su ma sun yi nuni da cewar mutanen da suka mutu za su iya fin mutane 769 din da Saudiyya ta ruwaito.

Turmutsutsun ya afku ne a lokacin da dumbun dubatar mahajjata suka cunkusu a wuri daya a hanyar ta zuwa jifan shaidan.

Mace-macen da kasashe suka sanar:

 • Iran: 464
 • Egypt: 75 , mutane 94 sun bace
 • Nigeria: 64 , mutane 244 sun bace
 • Indonesia: 57, mutane 78 sun bace
 • Mali: 60
 • India: 45
 • Pakistan: 40 , mutane 60 sun bace
 • Niger: 22
 • Cameroon: 45
 • Ivory Coast: 14 , mutane 77 sun bace
 • Chad: 11
 • Algeria: 11
 • Somalia: 8
 • Senegal: 10
 • Morocco: 10 , mutane 29 sun bace
 • Libya: 4 , mutane 16 sun bace
 • Tanzania: 4
 • Kenya: 3
 • Tunisia: 2
 • Burkina Faso: 1
 • Burundi: 1