Rasha ta kara zafafa hare-hare a Syria

Hakkin mallakar hoto SYRIA REBELS GATHERING
Image caption Wasu wuraren da jiragen yakin Rasha suka lalata a Syria

Kasar Rasha ta kara kai hare-hare ta sama a kasar Syria, tana mai cewa ta far wa yankunan mayakan IS.

Ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta Rasha ta ce jiragen yakinta sun kai farmaki kan wani wurin ajiye makamai da ke kusa da birnin Idlib, da kuma wani ginin rundunar mayakan IS mai hawa uku a kusa da birnin Hama.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na kasar Rashar.

Hukumomi a Syria sun ce taimakon da suke samu daga sojin Rasha ya kawo "babban sauyi" a yakin da ake yi.

Ana sa ran Amurka da Rasha za su yi wata tattaunawa ta musamman domin ka da dakarunsu su ci karo da juna a yakin da ake yi a Syria.