Mutane 15 sun mutu a hare-haren Abuja

Image caption Jami'an 'yan sanda a Najeriya

A Najeriya hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar ta ce mutane 15 ne suka mutu sakamakon wasu hare haren kunar bakin wake da aka kai wasu sassan Abuja babban birnin kasar a daren Juma'a.

Hukumar ta ce kimanin mutanen 40 sun jikkata sakamakon hare haren wadanda aka kai a Kuje da kuma Nyanya da misalin karfe goma na dare.

Alhaji Abbas Idris na hukumar bada agajin gaggawa a Abuja ya ce a Kuje, 'yan kunar bakin waken sun kai harin ne a wata kasuwa da kuma kusa da ofishin 'yan sanda inda mutane 13 suka mutu sannan 20 suka jikkata.

Ya ce mutun biyu ne suka mutu a harin na Nyanya sannan wasu 20 suka samu rauni, kuma an kai harin ne a kusa da babbar tashar motar da aka taba dasa bam a bara.