An hana tsaffin dalibai sa kakin soja a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin da ke yaki da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta haramta wa tsofaffin 'yan makarantar horon soja da ke Zaria, watau Nigeria Military School (NMS), sanya tufafin soja a tsakanin jama'a.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce, sanya kayan soja da tsofaffin daliban ke yi ya keta doka ne, kuma yana da munanan hadura ga martabar rundunar sojin kasar da kuma sanya kasar cikin matsalolin tsaro.

Sojojin sun umurci duk wadanda suka kammala makarantar bayan shekarar 2012 -- lokacin da aka fitar da ita daga cikin tsarin soja --da su tabbatar sun mayar da kayayyakin sojansu makarantar.

Rundunar ta jaddada cewa duk wanda aka samu da kayan soja ya karya doka, kuma za a hukunta shi daidai da yadda kundun tsarin mulkin kasa ya tanada.

A wani bangaren kuma, shugaban rundunar sojin kasa ta kasar, Laftanan-Janar Tukur Yusuf Buratai zai kaddamar da tsarin horo a barikokin sojin kasar baki daya ranar 5 zuwa 9 ga watan Otoba, inda za a bai wa iyalan sojoji tallafi na musamman wurin noma da ayyukan kasuwanci.