Shin karshen Boko Haram ya zo?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram sun kashe dubban mutane.

Najeriya ta yi hasashen cewa nan ba da dadewa ba za ta murkushe kungiyar Boko Haram, sai dai watakila dangatakar da kungiyar ta kulla da IS ta sa 'yan Boko Haram din su zafafa kai hare-hare a makwabtan Najeriya, kamar yadda wakilinmu a kan tsaro, Tomi Oladipo, ke cewa a wannan rahoton:

Rundunar sojin Najeriya tana ta hankoron ganin ta yi galaba a kan 'yan kungiyar Boko Haram a makonnin baya bayan nan.

Ta ce ta takura 'yan kungiyar, kuma nan gaba kadan za ta murkushe su - domin cika umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba ta na kawar da kungiyar cikin watanni uku.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau bai fito fili kamar yadda ya saba fitowa a bidiyo ba tun daga watan Fabrairu, lokacin da ya sha alwashin hana gudanar da zabukan kasar.

A watan Maris ne kuma Shekau ya ce kungiyar ta yi mubayi'a ga kungiyar IS, a wani sakon murya da ya fitar, kuma tun daga lokacin ya ja da baya.

Shekau ya sha fitar da sakonnin murya domin yin raddi ga rahotannin da ke cewa ya mutu, sai dai rashin fitowar sa fili ya sa sojoji na ta yin hasashen cewa sun kashe shi, kamar yadda suka sha fada.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta ce Boko Haram ta kusa zama tarihi.

Haka kuma, rashin fitowar sa fili ya sa kungiyar Boko Haram, wacce yanzu ake yi wa lakabi da kungiyar IS a yammacin Afirka, tana karbar umarni ne kawai daga manyan shugabannin IS.

Sai dai duk haka, a kwanan nan ya sake yin amfani da wata dama ta musanta ikirarin gwamnatin Najeriya, al'amarin da ya sa rundunar sojin kasar ta fahimci cewa wannan wasan buyan ba inda zai kai su.

Hakan ne ya sa kakakin rundunar sojin Najeriya Kanar Rabe Abubakar ya bayyana Shekau a matsayin wani mutum da ba shi da "muhimmanci" sannan ya yi kira ga 'yan kasar da kada su damu da sakonnin muryar da Shekau ke fitarwa, yana mai cewa yana yin hakan ne kawai ganin cewa "ruwa ya kusa karewa dan kada" .

A zahiri, farfagandar da 'yan Boko Haram ke watsawa ta ragu tun daga farkon wannan shekarar, lokacin da take amfani da hanyoyin sada zumunta na zamani wajen bayyana hotuna da bidiyon hare-haren da take kai wa.

Bidiyo na baya bayan da Boko Haram ta fitar, wanda ya zo daidai da lokacin da ake bukukuwan babbar Sallah, ba shi da inganci, kuma ya nuna mayakan kungiyar suna yin Sallah, sai dai da alama ba kwanannan aka dauka ba.

Shekaru biyu ke nan tun bayan da Amurka ta sa diyyar $7m ga duk wanda ya taimaka wajen kama Shekau, sai dai babu wanda ya iya kama shi, ko ma wani daga cikin manyan mayakan kungiyar.

Idan dai babu wanda ya kama Shekau, to kungiyar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta, ciki har da daukar sababbin mambobi da sake sababbin shirye-shirye na kai hare-hare.