'Yan Boko Haram 80 sun mika wuya

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption 'Yan Boko Haram su 80 har da kwamandojin su, sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan Boko Haram 80 sun mika wuya a garin Bama na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa na Najeriyar, Kanal Sani Usman Kuka-Sheka, ya shaida wa BBC cewa an tabbatar da cewa wadanda suka mika wuya suna da hannu a hare-haren da aka kai garin Bama.

'Yan kungiyar da suka mika wuya, inji kakakin rundunar sojin, wadanda suka hada da wasu kwamandoji da masu kai masu makamai da kuma mayaka, sun yi ba-ta-kashi da sojojin Najeriya, inda zafin da rundunar ta hada masu ya tilasta masu mika wuya.

Kanal Kuka-Sheka ya ce dakarun Najeriya a shirye suke su kawo karshen ta'addanci kafin lokacin da Shugaba Buhari ya kayyade masu ya cika.