Mace mai tuka motar marasa lafiya

Birnin Wajid da ke kasar Kenya ce tushen yakin da aka gwabza tsakanin Biritaniya da Italiya a yakin duniya na biyu, kuma a garin ne Bishara Farah, wata mata mai tuka motar ambulansa na daukar marasa lafiya zuwa wurare masu nisa.

Sunan Bishara ba bakon suna bane wurin marasa lafiyar da suka kunshi wadanda suka yi hatsarin mota, ko masu ciki ko ma masu fama da cizon dabbobi.

Bishara ta shafa fiye da shekaru biyu tana aiki a hukumar bayar da agajin gaggawa, inda ita kadai ce macce tsakanin su, kuma duk sun girme ta.

A kullum Bishara tana kutsawa cikin wurare da ke tattare da hadura a ciki da wajen birnin Wajid, inda ta ke ceto rayukan jama'a da dama, wadanda ta'addancin Al-Sabbab da kasar ke fama da shi ya shafa.

"Aiki na ya bukace ni da ceto rayukan mutane," In ji Bishara.

Ta kara da cewar "Saboda kullum ina yini da kunne daya a kasa domin sanni abin da ake ciki, saboda in yi saurin zuwa ceto rayuka."

An samu karuwar mace-mace a birnin Wajid, inda a bara Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewar an samu karuwar mutuwar masu juna biyu a duniya, kuma birnin Wajid ne na biyu a jerin garuruwan da suka fi yawan haka a Kenya.