Kun san dan bindigar da ya kashe mutane a Oregon?

Oregon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani da lamarin ya rutsa da shi a Oregon

Kafofin watsa labaran Amurka sun ce sunan dan bindigar da ya kashe mutane tara a makaranta Rosenburg a jihar Oregon, Chris Harper Mercer.

Dan bindigar -- mai shekaru 26 -- ya bude wuta ne a kan dalibai da safiyar ranar Alhamis kafin 'yan sanda su kashe shi bayan da suka yi musayar wuta.

Shugaba Obama -- wanda ya nuna alhini a kan lamarin -- ya roki Amurkawa da su dauki tsauraran matakai a game da takaita mallakar bindigogi.

Mr Obama ya ce nuna jimami kadai ga wadanda lamarin ya rutsa da su ba zai isa ba matukar ba a dauki matakai na hana aukuwar irin wannan danyen aiki da ke faruw akai-akai ba.

An kunna kyandira ta re da yin addu'o'i ga wadanda lamarin ya rutsa da su a garin Rosenburg.