Jirgin Amurka ya fadi a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Taliban ta ce ita ta harbo jirgin na Amurka.

Wani jirgin saman daukar kaya na Amurka ya fadi a kasar Afghanistan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 11.

Jirgin, mai suna C-130, ya fadi ne a filin jiragen sama da ke birnin Jalalabad na gabashin kasar, kusa da kan iyakar ta da Pakistan.

Wadanda suka mutu sun hada da ma'aikatan rundunar sojin Amurka guda shida da 'yan kwagila fararen hula guda biyar.

An fara gudanar da bincike kan dalilin hatsarin jirgin.

Wani kakakin kungiyar Taliban ya ce dakarunsu ne suka harbo jirgin, sai dai rahotannin da wasu kakafen watsa labarai suka bayar sun musanta hakan.