'A jakar leda aka ajjiye bam din kasuwar Kuje'

Kasuwar da bam ya tashi a garin Kuje
Image caption 'Yan sanda na bincike a kasuwar da daya daga cikin bama-baman Kuje ya tashi

Wani wanda ya shaida yadda bom din kasuwar Kuje ya tashi ya shaida wa BBC cewa wani mutum ne yazo a karamar mota fara kirar Nissan a inda ya nemi wasu mutane su uku masu sana'a da su ajjiye masa wani abu a jakar leda.

Jim kadan bayan tafiyarsa sai bom din ya tashi a inda mutane biyu daga cikin mutanen ukun suka mutu.

A daren Juma'a ne dai aka kai hare-haren da misalin karfe goma a kasuwar ta Kuje da ofishin 'yan sanda da kuma wata tashar mota.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce bayan an kwashe wadanda hare-haren Nyanya da Kuje suka shafa zuwa asibiti, an tabbatar da mutane 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da 41 suka jikkata.

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar Abuja, Ishaya Chonoko, ya yi karin bayani da cewa a Nyanya, mutane uku ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata; a Kuje kuma mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da 21 ke samun kulawa a asibitoci.

Mista Chonoko ya kuma ce Darakta Janar na hukumar Muhammad Sani Sidi ne ya jagoranci kwashe mutanen da abin ya shafa. Tuni dai gwamnati ta ce ta dauki nauyin biyan kudin asibitin.

Ita kuwa hedkwatar rundunar 'yan sanda ta Najeriyar cewa ta yi binciken farko da ta gudanar ya nuna cewa 'yan kunar-bakin-wake biyu ne, mace da namiji, suka kai hare-haren.

Rundunar 'yan sandan, a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai magana da yawunta, ACP Olabisi Kolawole, ta ce tuni Sufeto Janar na 'yan sanda Solomon Arase ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen yankin na Babban Birnin Tarayya, FCT.