Kasa ta binne mutane a Guatemala

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ruwan kamar da bakin kwarya na haifar da faruwar zaizayar kasa da kan binne gidaje ya kuma hallaka jama'a

Masu ceto a Guatamala sun yi amanna cewa Mutane fiye da 350 ne ke binne a karkashin baraguzan gine-ginen da suka fadi a sakamakon zaizayar kasar da ta afku a ranar Alhamis a kasar.

Sama da gawawwaki 73 ne masu aikin ceton su ka gano kana kuma an ceto kimanin mutane 30 da ke da sauran shan ruwa.

Tan tan na duwatsu da tabo ne su ka binne gidaje da yawa a yayin da wani yankin gandun daji da ke bakin wani tsauni ya zabtaro a sakamakon wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya.

Masu aikin ceto na amfani da manyan injina da kuma karnuka domin ceto wadan da su ka makale a karkashin baraguzan gine-ginen.

Daya daga cikin jami'an da ke jagorantar gudanar da aikin ceton ya ce muna sa ran ceto wasu karin mutane da hadarin ya shafa.

Za a ci gaba da gudanar da bincike ne guda biyu watau na daidaikun mutane da kuma na amfani da manyan injina da za a yi amfani da su wajen ture kasa.

Mutane sun yi wani dogon layi a kofar wani dakin ajiye gawawwaki na gaggawa da aka yi a in da su ke kokarin shaida 'yan uwansu da suka mutu.

Aikin ceto a yankin na cin karo da canjin yanayi da kuma yiwuwar sake wani ruwan sama mai kamar da bakin kwarya.