An soma gasar gashin baki da gemu ta duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu shiga gasar na tara gashin baki tsawon lokaci tare da kulawa da shi domin su samu nasara

Masu gasar tara gashin baki da gemu daga kasashe 20 sun taru a birnin Leogang na Austria domin shiga gasar tara gashin baki da gemu ta duniya.

Yawancin wadanda suka shiga gasar daga Jamus da Austria su ke.

Rukunan gasar 18 ne -- ciki sun hada da gemun da ya fi kowanne yawa, da shagiri da kuma gemun da ya fi kowanne ban sha'awa.

Wasu mutane ne aka zaba na musamman domin yin alkalanci a gasar wacce a karshe za a fitar da gwani na gwanaye na duniya.