Sojojin Amurka ne su ka kai hari Kunduz

Hakkin mallakar hoto MSF
Image caption Asibitin Kunduz

Shugaba Obama ya bayyana jimami tare da ta'aziyyar sa ga iyalan wadan da su ka rasa rayukan su sakamakon hari ta sama da aka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 a asibitin Kunduz da ke arewacin Afghanistan.

Sai dai kuma shugaban ya ce zai jira sakamakon bukatar da ma'aikatar tsaron Amurka ta gabatar kafin yanke hukunci akan abin da ya faru.

Sojojin Amurka sun amince da zargin da a ke yi musu na kai harin jiragen saman yaki a yankin da wani asibiti yake a Kunduz da ke Aghanistan.

Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce sun yi niyyar kai hari akan masu tayar da kayar baya ne ba asibitin ba.

Daraktan kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontiers Bart Janssens ya ce dole a gudanar da bincike dangane da harin.