Boko Haram ta dauki alhakin harin Abuja

Image caption Jami'an tsaro su na gudanar da bincike a inda bam ya tashi

Mayakan da ke ikirarin kasancewa 'yan kunigyar IS reshen Afrika ta yamma ko kuma Boko Haram kamar yadda ake kiran su sun ce su ne suka kai harin bama bamai a wasu yankunan Abuja, babban birnin Najeriya.

Kungiyar -- wadda ake yi wa lakabi Jamhuriyar Islama a yammacin Afirka -- ta wallafa hotunan mambobinta uku da ta ce su ne suka kai hare-hare a Nyanya da Kuje, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 18.

'Yan sanda dai sun ce sakamakon kwarya-kwaryar binciken da suka yi ya nuna cewa 'yan kunar-bakin-wake guda biyu ne suka kai hare-hare -- mace da namiji.

Shugaban Najeriya, wanda ya ziyarci mutanen da suka samu raunuka sakamakon hare-haren a babban asibitin kasa da ke Abuja, ya bukaci jami'an tsaron kasar su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu.

Ya nanata alwashin da ya sha na murkushe kungiyar Boko Haram nan ba da dadewa ba.