Dalibai a Kenya sun koma makaranta

Image caption Dalibai sun soma daukar darasi bayan yajin aiki mai tsawo

Miliyoyin dalibai a Kenya sun koma makaranta bayan da malamansu suka janye yajin aiki na makonni biyar saboda batun karin albashi.

Kungiyoyin malaman sun ce sun janye yajin aikin ne domin yin biyayya ga umarnin kotu, wacce ta bai wa malaman da gwammnatin Kenya kwanaki 90 domin su warware takaddamar da ke tsakaninsu a kan biyan albashi.

Takaddamar dai ta barke a tsakanin bangarorin biyu ne saboda umarnin da kotun kolin kasar ta bai wa gwamnatin ta biya malaman karin kashi 50 na albashi, ko da ya ke gwamnatin ta ce ba za ta iya biya ba.

Hakan ne ya sa malaman suka shiga yajin aiki, inda suka kulle dukkan makarantun gwamnatin kasar.

Yanzu dai fiye da yara miliyan daya -- wadanda ake sa ran za su rubuta jarrabawa a wannan watan -- sun koma makaranta, sai dai malaman ba su fara koyar da su ba.

Malaman sun bukaci malaman makarantu masu zaman kansu da su shiga yajin aikin, sai dai sun ki yarda, kuma an bar su sun ci gaba da koyarwa.