Yadda shirye-shiryen rediyo ke jan hankula

Image caption Idris Sada Kurfi ya ce baya fita daga gidansa kullun safiya sai ya ji shirin

Rai dangin goro, wani shiri ne da ake gabatarwa a gidan rediyon Express da ke watsa shirye-shiryensa ta zangon FM a Kano.

Ba wani sabon abu shirin ya zo da shi ba, don ko a baya a kan karanta littafin Hausa ko littatafan soyayya kamar yadda aka fi saninsu a radio, wadanda yawanci marubuta ke rubutawa kan yanayin zamantakewar Hausawa da soyayya tsakanin ma'aurata da sauran matsalolin rayuwa.

Sai dai wannan ya sha bamban ta salon gabatar da shi, ta yadda makarancin ke sauya murya a duk sanda zai yi maganar namiji ko mace.

A iya cewa wannan shiri yana cin zamaninsa, ganin yadda a sassa da dama na birnin Kano, daga karfe 9.30 zuwa karfe 10 na safe, mutane ke raja'a wajen sauraransa, walau a gidaje ko kasuwanni ko asibitoci ko a kan tituna kai har ma da makarantu.

Image caption Ma'abociya jin shirin Hajiya Innarmu ta ce da wayarta ta ke sauraron shirin

Wata ma'abociyar shirin, Maman Muhammad, kamar yadda ta bukaci a kirata ta ce shirin yana da tasiri a zukatan mutane.

Ta ce "shirin ya karbu fa sosai a wajen mutane. Akwai wani asibiti da na ke zuwa awon ciki, idan mata suka taru to ma'aikatan asibitin ma ba sa fara yin awon sai mun gama jin shirin. Kuma ni ina jin shirin ne saboda ina karuwa sosai ta fuskar zamantakewar rayuwa."

Shirin rai dangin goro ya yi tasirin da ba wai hankalin mata kawai yake ja ba kamar yadda aka san ire-irensa na yi, har maza magidanta ma ba a bar su a baya ba. Su ma su kan yi zaman sauraren shirin a kasuwa ko majalisa ko ma tare da iyalansu.

Yadda wasu ke ganin cewa shirin ya samu karbuwa a zukatan al'umma yara da manya, maza da mata a jihar Kano, shi ne ya sa Malaman addini suka shiga fadakarwa a masallatai da wuraren wa'azi, cewa shirye-shirye makamantan wannan suna bata tarbiyyar jama'a a maimakon gyara.

Sheikh Abdulmudalib Ahmad Muhammad shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Jibril Umar Jibril da ke Fagge, wanda yake kallon wannan shiri a matsayin wata jarrabawa mai muni da al'umma suka samu kansu a ciki.

Ya ce "sau biyu muna huduba a masallacin nan muna jawo hankalin masu yin wannan shiri da cewa su dubi girman Allah su dinga watsa shirye-shirye masu ma'ana ba wadanda za su bata tarbiyar jama'a ba."

Image caption Farfesa Yusuf Adamu, ya ce shirin ci gaba ne ga al'umma

Sai dai wani manazarci Farfesa Yusuf Adamu, tsohon shugaban kungiyar marubuta ta Najeriya, na ganin wannan wani ci gaba ne da al'umma ta samu.

"Ai kamar yadda sunan shirin yake "rai dangin goro ne" yana son nishadi, don haka ni ban ga wata illa da wannan shiri ke da ita ba," in ji shi.

Sai dai kuma ba a taru an zama daya ba, wata Malamar makaranta da ke matukar adawa da wannan shiri ta ce, "Na taba kama wata yarinya a aji ina koyarwa ashe ita ta makala waya a kunne tana ta faman sauraran wannan shiri. Gaskiya akwai illa ga tarbiyyar yara wajen sauraran shirin."

Mai gabatar da shirin, Ahmad Isah, wanda ya shafe shekaru da dama yana wannan aiki, ya shaida bayyana yadda yake ji da sukar da shirin ke sha. "Ni bana ja in ja da Malamai masu cewa wannan shiri bai dace ba, abinda nake so a sani shi ne bani ke da gidajen rediyon ba, kuma bani ke rubuta labarin ba. Bayan haka ma akwai shirye-shirye irin wadannan da dama amma sam ba a magana a kansu sai wannan. Watakila don ya fi jan hankalin mutane ne."

Ganin yadda wannan shiri ya damfaru a zukatan jama'a ya sa, abokiyar aikinmu ta sake tambayar ma'abota shirin ko idan aka wayi gari an dakatar da shi ya za su ji?

Wani magidanci Alhaji Idris Sada Kurfi sai ya ce, "Gaskiya idan aka hana watsa wannan shiri, mu masu hawan jini aka cuta, don kuwa yana debe mana kewa ba kadan ba."

Ga alama dai tasirin da shirin yake da shi ya jawo gasa a tsakanin gidajen rediyon da ke Kano, don kuwa a baya-bayan nan gidan ma rediyon Freedom ya bi sahu.