Sojojin Isra'ila sun kashe Bafalasdine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zaman dar-dar tsakanin Falasdinawa da 'yan Isra'ila

Wasu majiyoyi a Falasdinu sun ce sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine matashi a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da Bethlehem.

Wannan shi ne Bafalasdine na biyu da sojin Isra'ila suka kashe cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

Isra'ila ta kara tsaurara matakan tsaronta tun bayan da aka kashe wasu Isra'ilawa hudu a wasu hare-hare da Falasdinawa suka kai a 'yan kwanakin da suka wuce.

Bayan kashe-kashen an rufe yawancin zuwa tsohon birnin Kudus ga Falasdinawa a rana ta biyu a jere, a wani mataki da ba'a taba ganin irinsa ba.