Red Cross ta janye daga Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Red Cross na taimako a fadin Afrika

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross ta janye ma'aikatanta daga wani gida da take ajiye kayayyakin agajinta a Sudan ta Kudu.

Hakan ya faru ne bayan da wasu mutane dauke da makamai suka kwashe kayan.

Cikin wata sanarwa, kungiyar ta Red Cross ta ce a karshen mako ne gwamman 'yan bindiga suka shiga sansanin da ke karamar hukumar Leer a jahar Unity suka sace kayayyakin aikinsu da magunguna da kuma kudi sannan muka suka razana ma'aikatanta.

A watan jiya ne kungiyar ta koma aiki a wajen tun bayan da ta fice a watan Mayu sakamakon fadan da ake a can.

Tuni aka soke rarraba abincin da za a yi a wannan watan.