Turkiya ta tsare jirgin yakin Rasha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rasha ta ce ta shiga Syria ne domin yaki da 'yan tawaye

Turkiya ta bayyana matukar rashin jin dadinta ga mahukunta a Moscow bayan da ta tsare wani jirgin yakin kasar Rasha da ya keta sararin samaniyarta ba bisa ka'ida ba, kusa da kan iyaka da Syria.

Turkiyar ta ce ta tashi jiragen yaki biyu wadanda suka tsare jirgin na Rasha a ranar Asabar.

Rasha ta bayyana kutsen da ta yi cikin sararin samaniyar Turkiyar da cewa kuskure ne na na'urar da ke nuna taswirar hanya.

Kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana kutsen a matsayin abin da baza a lamunta ba kuma tana shirya yin wani taron gaggawa da dakarun kawancen.

Turkiyya ta ce a shirye ta ke ta dauki mataki idan har aka kara keta dokokin sararin samaniyarta.