Mutane 16 sun mutu a harin bam a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan kunar-bakin-waken ya tashi bam a kusa da wasu mutane da ke yin hira.

Mazauna birnin Damaturu na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce mutane 16 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai a birnin.

Ganau sun shaida BBC cewa lamarin ya auku ne a wurare biyu.

Na farko, wani dan kunar-bakin-wake ne ya tashi bama baman da ke jikinsa a kusa da wasu mutane da ke hira, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sa da mutane uku.

Na biyu kuma ya faru ne lokacin da wani dan bindiga ya tara mutane 'yan gida daya a wata rugar Fulani domin ya yi musu wa'azi, amma sai ya kashe dukkan su guda goma.

Garin dai ya sha fama da hare-haren kungiyar Boko Haram.