'EFCC na binciken na hannun damar Diezani'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana binciken Diezani a London

Hukumar yaki da rashawa ta Nigeria, EFCC ta damke Jide Omokore, daya daga cikin shugabannin kamfanin Mai na Atlantic Energy. Ana yiwa Jide Omokore kallon na hannun damar tsohuwar ministar mai, Diezani Alison-Madueke.

Hukumar EFCC na binciken Omokore ne bisa zargin hallata kudaden haramun da kuma hada baki wajen wawure kudaden kwangiloli na mai a lokacin da Diezani ta ke minista.

A kwanakin baya, kamfanin Atlantic Energy ya wallafa wani martani a jaridar Premium Times ta Nigeria inda ya ke musanta aikata ba daidai ba.

Wasu bayanai sun ce EFCC ta gudanar da bincike a gidan Omokore da ke Lagos da kuma gidan tsohuwar ministar a Abuja.

Wata majiya ta ce wannan kamu ba zai rasa nasaba da binciken da hukumar kula da manyan laifuka ta Birtania ta ke yi ba akan zargin halatta kudaden haram.

Tuni dai hukumar ta NCA ta fara bincike inda ta kama mutane hudu a birnin London, wadanda suka hada da tsohuwar ministar albarkatun Mai ta Nijeriyar, Misis Diezani Alison-Madueke.

A ranar Litinin wata kotun Majistire a Westminster da ke London ta amince wa hukumar binciken manyan laifuka ta Biritaniya, NCA ta rike fam 27,000 da aka samu a hannun tsohuwar ministar mai ta Nigeria, Diezani Alison-Madueke.