NATO na fushi da Rasha kan kutse a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jens Stoltenberg ya ce da gangan Rasha ta yi kutse a Turkiyya.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO ya yi Allah-wadai da kutsen da jiragen yakin Rasha suka yi zuwa cikin Turkiya, yana mai cewa abu ne da ba za a amince da shi ba.

Jens Stoltenberg ya ce Rasha ba ta bayar da gamsasshen bayani ba a kan dalilan da suka sa ta yi kutse cikin kasar ta Turkiya, yana mai cewa da alama da gangan ta yi hakan.

Sau biyu jami'an Turkiyya suka gayyaci jakadan Rasha da ke kasar a kan lamarin, kuma sun yi masa gargadi cewa duk jirgin da ya sake yin kutse a cikin kasarsu, zai fuskanci fushin kasar.

A karshen makon jiya ne dai jiragen Rasha suka yi kutse cikin sararin samaniyar Turkiyya, cikin su har da jiragen da ke kai hare-hare a Syria.

Mista Stoltenberg ya soki Rasha saboda hare-haren da ta kai, yana mai cewa ya kamata a rika kai wa 'yan kungiyar IS, ba 'yan hamayyar Syria da fararen hula ba.