Mutane sun rasa muhallansu a Mangu

Dubban mutane a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau sun rasa muhallansu bayan sakamakon tashin hankali mai nasaba da addinni da kabilanci.

Rahotanni na cewar kusan mutane 30 ne suka rasa rayukansu a yayin da aka lalata dukiyoyi na al'umma a kauyukan Mangu din sakamakon tashin hankali.

Tuni da mutanen da suka rasa muhallansu suka nemi mafaka a wasu wurare domin tsira da ransu.

An dade ana fama da tashin hankali mai nasaba da addini na kabilanci a jihar Plateau inda aka yi hasarar rayukan mutane da dama.

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya yi alkawarin kawo karshen tashin hankali da yaki ci yaki cinyewa a jihar.