Shin su wanene sabbin ministocin Nigeria?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bukola Saraki ne ya bayyana sunayen ministocin a zauren majalisar dattawa.

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bayyana sunayen mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar domin nada su a mukaman ministocin.

Majalisar dattawan ta tsayar da ranar 13 ga watan Okotoba a matsayin ranar da za ta soma tantance ministocin.

Sunayen sun hada da:

Hakkin mallakar hoto AFP

1. Babatunde Fashola, Ya yi gwamnan jihar Lagos daga shekarar 2007 zuwa 2015. Dan shekaru 52, Fashola lauya ne kuma ya taba rike mukamin shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin jihar Lagos a zamanin mulkin, Bola Ahmed Tinubu.

2. Cif Audu Ogbeh, daga jihar Benue. Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne kuma ya taba rike mukamin ministan sadarwa a zamanin mulkin shugaba Shehu Shagari. Ogbeh mai shekaru 68, ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.

3. Hadi Sirika, tsohon Sanata ne daga jihar Katsina. Kuma ya taba zaman dan majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007. Sirika tsohon matukin jirgin sama ne.

4. Abubakar Malami SAN, Babban lauye ne kuma ya taba rike mukamin shugaban kula da bangare shari'a na tsohuwar jam'iyyar CPC ta shugaba Buhari.

5. Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya shafe shekaru hudu a kan kujera kafin ya sha kashi a lokacin yana neman wa'adin mulki na biyu. Inda Ayo Fayose na jam'iyyar PDP ya samu galaba a kansa.

6. Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Rivers daga 2007 zuwa 2015. Dan jam'iyyar PDP ne kafin ya sauya sheka ya koma APC. Shi ne ya jagoranci yakin neman zaben shugaba Buhari.

7. Udoma Udoh Udoma, tsohon Sanata ne daga jihar Akwa Ibom daga shekarar 1999 zuwa 2007 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP. Ya yi takarar gwamna amma bai samu nasara ba.

8. Ahmed Musa Ibeto, tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger daga shekarar 2007 zuwa 2015. Ya raba gari da tsohon mai gidansa, Muazu Babangida Aliyu, shi ne yasa ya bar jam'iyyar PDP ya koma APC.

9.Kemi Adeosun, tsohuwar kwamishiniyar kudi ce a jihar Ogun. Ta karanta fannin tsimi da tanadi a Ingila kuma ta shafe fiye da shekaru 23 tana aiki a fannin tattalin arziki.

10. Suleiman Adamu - dan jihar Jigawa ne. Kuma Injiniya ne wanda ya shafe shekaru yana aiki. Dan Sarkin Kazaure ne kuma ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya da kuma jami'ar Reading ta Ingila. Adamu ya yi aiki da Afri Projects kamfanin da ke lura da kwangilolin PTF.

Hakkin mallakar hoto NNPC Website

11. Emmanuel Kachikwu, shi ne shugaban kamfanin mai na Nigeria NNPC. Dan jihar Delta ne kuma tsohon ma'aikacin Exxon Mobil ne wanda ya karanta fannin shari'a a jam'iyyar Nsukka.

12. Janar Abdulrahman Dambazau, tsohon babban hafsan sojin kasa a Nigeria. Dambazau dan jihar Kano ne kuma yana da digirin-digirgir.

13. Aisha Alhassan, ta yi takarar gwamna a jihar Taraba amma ta sha kaye a hannun Darius Ishaku na jam'iyyar PDP. 'Yar majalisar dattijai ce daga 2011 zuwa 2015 an zabi Aisha Alhassan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kafin ta koma APC.

14. Lai Mohammed, tsohon kakakin jam'iyyar APC ne daga jihar Kwara. Kuma tsohon ma'aikacin hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nigeria ne watau FAAN.

15. Chris Ngige, tsohon gwamnan jihar Anambra ne kafin ya sha kaye a kokarin tazarce inda Peter Obi na jam'iyyar APGA ya samu galaba a kansa. Ngige ya yi Sanata daga 2011 zuwa 2015.

Hakkin mallakar hoto Getty

16. Amina Ibrahim, tsohuwar mai bai wa shugaban Nigeria shawara a kan harkokin muradun karni a zamanin mulkin Cif Obasanjo da kuma marigayi Umaru Yaradua. Ta yi aiki tare a ofishin babban sakatare na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon.

17. Ogbonnaya Onu, shi ne gwamna na farko a jihar Abia daga 1992 zuwa 1993. Ya taba rike mukamin shugaban jam'iyyar ANPP na kasa kafin kafa jam'iyyar APC. Onu ya yi karatu a jami'ar Lagos da kuma ta California a Amurka.

18. Solomon Dalong, dan jam'iyyar APC ne daga jihar Filato. Ya yi takarar gwamna amma Simon Lalong ya doke shi a zaben fitar da gwani.

19. Adebayo Shittu, dan jihar Oyo ne. Kuma ya yi takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar CPC a shekara ta 2011 inda Abiola Ajimobi na jam'iyyar ACN ya samu galaba a kansa. Shittu kwararren lauye ne.

20. Osagie Ehanire, dan jihar Edo ne. Shi ne shugaban gidauniyar TY Danjuma kuma kwararren likita ne wanda ya shafe shekaru yana aiki a babban asibiti na gwamnatin tarayya da ke Benin.

21. Ibrahim Usman Jibril, dan jihar Nassarawa ne.