Jirgin sama sun yi kira ga ma'aikata su ajiye aiki

Wani jirgin sama mara matuki ya jefo takardu daga sama a sansanin sojin Amurka da ke kusa da birnin Frankfurt da ya yi kira ga ma'aikatan Hukumar tsaro ta kasar su sama da dubu daya a kan su ajiye aikinsu.

Wata kungiya da aka dora wa alhaki, da ake kira Intelexit, ta ce manufarta ita ce ta fadakar da ma'aikata a kan bukatar ganin cewa sun goyi bayan shirye -shiyen leken asiri da kuma hare haren da jiragen sama mara matuka suke kai wa.

Kakakin kungiyar ta Intelexit ,sascha Fugel ya ce san san cewa akwai wasu ma'aikata a sansanin da suka shiga yanayi na tsaka mai wuya saboda rawar da suka taka wajen leken asiri.

A cikin sansanin akwai wata cibiya ta musaman da aka kafa da ke nazari kan abubuwa da suka shafi lisafi a kasar Jamus.

Sai dai hukumar tsaro ta Amurka ta ce tana bin kaidoji a cikin ayuikanta.