Za a samu tururuwar 'yan gudun hijirar Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijira da yawa sun tsallaka zuwa Turkiyya kan hanyarsu na zuwa Turai.

Shugaban Majalisar Tarrayar Turai Donald Tusk, ya ce Turkiyya ta gargadi EU cewa za a iya samun karin tururuwar 'yan gudun hijira daga kasar Syria sakamakon yaki da ya tsananta.

Shugaban ya kara da cewa hadin gwiwar kasashen Rasha da Iran a yakin Syria, na bai wa Shugaba Bashar al-Assad damar samun nasara.

Turkiyya ta kiyasta tururuwar za ta kai mutane miliyan uku, kuma duk daga garin Aleppo ne.

A wani bangaren kuma, Hukumar kula da kaurar jama'a watau International Organization for Migration (IOM), ta kasa da kasa ta ce bata da labarin cewar jama'a na barin Syria.

Rahotanni da IOM ta fitar ta samu tabbaci ne daga kungiyar agajin gaggawa ta Red Cross Crescent, da ke nuna cewar daruruwan 'yan gudun hijira ne suka mutu a tekun Bahar Rum da ke kusa da Libya tun ranar Lahadi.

An gano gawar wani mutumi da ake zaton dan kasar Eritrea ne a ranar Litinin, bayan da gobara ta barke a wani sansanin da aka kebe wa masu neman mafaka a gabashin kasar Jamus.

'Muna bukatar Turkiyya'

A wani taron majalisar Turai, Mista Tusk ya ce, "A lokacin wani ziyara da na kai yankin, duk wanda na tattauna da su a Turkiyya da Jordan da Masar, sun yi min gargadin cewa akwai alamun nasara a mulkin Assad, musamman saboda hadin gwiwar Rasha da Iran a Syria, hakan kuma zai yi sakamakon tururuwar 'yan gudun hijira."

Rasha ta soma kai farmaki Syria a ranar 30 ga watan Satumba, inda ta ce Shugaba Assad ne ya bukace ta da kai wa kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci, watau IS hari, duk da cewar sun musanta zargin da Rasha cewar hare-haren na shafar fararen hula.

A kasar Brussels, an gudanar da wani taro, inda Shugaban kasar Turkiyya, Mista Erdogan da shugabannin Tarayyar Turai suka amince da cewar za su nemi cimma matsaya cikin 'yan kwanakin nan, game da matsalar 'yan gudun hijira.

Daruruwan 'yan gudun hijira, da suka fito daga Gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika, inda yaki ya tsananta, sun iso Turai wannan shekarar, kuma a watan da ya gabata ne EU ta tsara wasu matakai na samar wa 120,000 daga cikin su muhalli cikin shekaru biyu.