Ana tuhumar jami'in MDD da cin hanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Batun cin hanci ya dabaibaiye Ashe

An tuhumi tsohon shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya, John Ashe, da wani zargi da ya shafi cin hanci.

Hakanan kuma an tuhumi wasu mutane biyar a kan wannan zargi.

John Ashe, wanda jakadan Majalisar Dinkin Duniya ne daga Antigua da Barbuda--shi ne shugaban babban taron MDD a shekara ta 2013.

Ana zargin sa da karbar cin hanci na sama da dala miliyan daya da dubu dari uku daga wasu 'yan kasuwar China.

Inda aka yi zargi shi kuma ya yi amfani da mukaminsa ya taimaka mu su ta fuskar kasuwancinsu.

Har ila yau ana zargin ya karbi kudi domin kai iyalinsa hutu da kuma gina wajan wasan kwallon kwando a gidansa.

Sakataran MDD, Ban Ki Moon ya ce ya yi matukar kaduwa da jin wadannan zarge zarge.