Shugaban Volkswaja ya sha alwashin gyara

Image caption Kamfanin ya shiga tsaka mai wuya

Sabon shugaban kamfanin kera motoci na Volkswaja ya yi gargadin cewar abun kunyar nan na magudi wajen rage yawan hayakin da motocin ke fitarwa zai haifar da mummunan sakamako ga kamfanin.

Mathias Mueller ya shaidawa wani taro na ma'aikatan kamfanin su kusan dubu ashirin cewar kudaden da aka ware, watau Euro biliyan shida da rabi domin asarar da aka tafka ba za su isa ba.

Ya ce a yanzu haka ana yin nazari a kan duk wani shiri na kashe kudade, kuma duk abun da aka ga bai zama wajibi ba za a dakatar da shi ko a soke shi baki daya.

Ya kara da cewa zai yi iya bakin kokarinsa ya kare guraben aikace-aikacen yi, amma ya amsa cewar lalle ba za a yi sauye-sauye ba, ba tare da sun yi illa ba.