'Yan fashi sun mamaye wani gari a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Hakkin mallakar hoto zamfara website
Image caption Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari

A Najeriya, rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wasu 'yan fashi sun mamaye wani kauye da ake kira Maberaya, a karamar hukumar Shinkafi a yammacin jiya inda rahotani ke cewa sun ci karansu babu babbaka.

Wasu mazauna kauyen da suka tsere bayan barayin sun yiwa kauyen dirar mikiya sun shaidawa BBC cewa dukkanin mutanen kauyen ne suka fice daga cikin garin saboda fargaba.

To sai dai mun kita kakakin rundunar yan sanda ta jihar Zamfara DSP Sanusi Amiru ta wayar tarho amma wayar tasa ta rika kuka ba bu wanda ya amsa mana.

Jihar Zamfara dai na fuskantar barazana daga 'yan fashi da makami wadanda a wasu lokutan su kan janyo asarar rayuka da kuma ta dukiyoyi.