Boko Haram ta kalubalanci sojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Screengrab
Image caption Ba a nuna Shekau ba a bidiyon

Kungiyar Boko Haram ta fitar da sabon faifan bidiyo, inda wani wanda bai bayyana ko shi wanene ba, ya kara jaddada mubaya'arsu ga kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci, watau IS.

Ya kara da cewa kungiyar ta IS a yammacin Afrika har yanzu tana karkashin shugabancin Abubakar Shekau.

Sai dai ba kamar a baya ba, Shekau bai bayyana a wannan sabon faifan bidiyo ba.

Wannan ne bidiyo na uku kenan da wasu ke magana da yawun kungiyar Boko Haram wanda ba Abubakar Shekau bane.

Mai bayanin ya yi ne da harsunan larabci da Hausa, ko da yake ba bahaushe ba ne, inda ya musanta ikirarin rundunar sojin Najeriya cewa wasu daga cikin 'yan kungiyar sun mika wuya ga sojoji.

Ya kuma musanta cewar sojojin sun ceto mata da yara da 'yan kungiyar suka sace, kuma ya zargi rundunar sojin Najeriya da amfani da kafofin watsa labarai domin nuna wa duniya abin da ba shi ne ba, inda ya jaddada cewar kungiyar tana kan bakan ta na ci gaba da gwagwarmaya.