Me ya bambanta ministocin Buhari da na baya?

Hakkin mallakar hoto
Image caption Buhari ya san halayyar ministocin da ya zaba

Masu lura da al'amuran siyasa a Najeriya na cewa mutanen da shugaba Muhammadu Buhari yake shirin yin aiki da su a matsayin ministoci sun bambanta da na gwamnatocin baya.

Dr Abubakar Kari, malami a Jami'ar Abuja ya ce babban abin da ya bambanta ministocin da Buhari ya mika sunayen su da na gwamnatocin baya shi ne dukkannin su ba baki ba ne a gare shi.

Ya ce sabanin ministocin Obasanjo da Umaru 'Yar'adua da kuma Goodluck Jonathan suka dauka wadanda kusan dukkannin su baki ne a gare su.

Hakan ne ma ya sa Dr Kari yake ganin shi ne ummul-abaisin samun matsaloli a gwamnatoci na baya.

Ya kuma kara da cewa zai yi wuya a samu matsala tsakanin Shugaba Buhari da ministocinsa tunda sun san halayensa da akidarsa kuma ba za su nemi saba masa ba.

A ranar Talata ne dai shugaban majalisar dattawan Najeriya ya karanto jerin sunayen ministocin da shugaba Buhari ya aike wa da majalisar.