Buhari ya gana da Saraki da Dogara

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri a daren Laraba da shugabannin Majalisun dokokin kasar a fadarsa da ke Abuja.

Babu dai wani cikakken bayani kan makasudin wannan ganawar, amma ta zo ne kwana daya bayan da majalisar dattawan kasar ta soma shirye-shiryen tantance mutanen da shugaban ya mika mata domin zaman ministoci.

Ganawar wadda aka fara da misalin karfe tara na dare, ta gudana ne tsakanin Shugaban Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatinsa Babacir David Lawal a bangare daya .

A dayan bangare kuma akwai shugaban majalisar dattawan kasar Abubakar bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da sauran shugabannin majalisun biyu .

Bayan fitowa daga ganawar Shugaban Majalisar dattawan, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ce zama ne kawai suka yi na musayar ra'ayoyi tsakanin bangarorin zartarwa da yin dokoki na kasar bisa gayyatar shugaba Buhari.

Sai dai masu lura da al'amura na ganin wannan ganawar na iya zama wani kokari na kawar da kallon-hadarin-kaji da ake yi wa juna tsakanin fadar shugaban kasar da jam'iyyar APC mai mulkin kasar da kuma majalisun dokokin.