Burkina Faso: Za a hukunta Diendere

Hakkin mallakar hoto
Image caption Janar Diendere, madugun masu juyin mulki a Burkina Faso

Hukumomi a Burkina Faso sun kama madugun da ya jagorancin juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata, janar Diendere, da laifuka har 13.

Laifukan guda 13 sun hada da na kisan kai da yi wa sha'anin tsaron kasa barazana da kuma lalata kayayyaki bisa keta.

Wata kotun sojoji ce ta musamman za ta yanke masa hukunci.

An kuma samu wani tsohon ministan wajen kasar, Djibril Bassole da laifin hada baki da sojojin kasashen waje wajen tayar da yamutsi a kasar.

A wata Satumba ne dai Janar Dienere wanda shi ne shugaban masu tsaren fadar shugaban kasar ya jagoanci juyin mulki kafin daga bisani kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS ta shiga al'amarin.

Kafin ya yarda ya sauka daga kujerar dai, janar Diendere ya nemi da ayi alkawarin ba za a hukunta su ba.