Ministocin NATO na yin taro a kan Rasha

Jirgin sama Rasha Hakkin mallakar hoto Russian Ministry of Defence
Image caption Jirgin sama Rasha

Ministocin tsaro na kungiyar kawance ta NATO za su yi taro ranar Alhamis a Brussels domin tattauna wa kan yadda Russia ke matsa kai hare-haren soji a Syria.

Hankali dai ya fara tashi ne a tsakanin kasashen kungiyar tun bayan da Turkiyya ta koka cewa jiragen yakin kasar ta Russia sun keta sararin samaniyarta.

Ana tsammanin cewa ministocin za su mara wa Turkiyya baya ne da kuma shelar kare duk wata kasa mamba a kungiyar.

Za kuma su tattauna a kan rikicin Ukraine.

Wakilin BBC ya ce taron yana nuni da cewa Russia ta shiga taitayinta domin kungiyar za ta iya amsawa da chas da zarar Russiar ta ce kule.