Toyota zai fito da mota mai tuka kanta

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Mota mai tuka kanta

Kamfanin kera motoci na Toyota zai fara gwajin mota mai tuka kanta a kan tituna.

An dai yi gwajin motar kirar Lexus GS a kan babban titin Shuto da ke Tokyo.

Kuma motar ta nuna halayya irin ta wadda mutum yake tukawa kamar yin kwabo da sauya hannu da kuma ba wa sauran motoci tazarar da ake bukata.

Kamfanin na Toyota ya ce yana fatan kaddamar da irin wadannan motoci a shekarar 2020 a dai-dai lokacin karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta duniya wadda Tokyo za ta yi.

Ita dai wannan motar marar matuki kamar yadda kamfanin na Toyota ya ce tana amfani da wasu fasahohi masu gane motocin da ke kusa da su sannan kuma suna iya sauya hannu ko hanya idan akwai yiwuwar hakan.

Ta amfani da wadannan tarin fasahar ne motar take iya jujjuya kan motar wato steering da karawa ko rage gudu har ma da taka birki kwatankwacin yadda dan adam yake sarrafa mota.

Wannan matsayin ya sanya kamfanin na Toyota ya zamo na farko da zai dora mota mai tuka kanta a kan titi.

A makon da ya gabata, kamfanin General Motors ya ce zai yi wa ma'aikatansa da ke wurin aiki na Warren a Michigan, ababan hawa masu tuka kansu.

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kamfanin Toyota zai kaddamar da motar a 2020

Kamfanin Nissan ma ya yi alkawarin sanya motocin masu tuka kansu a kan titunan kasar Japan a shekarar 2016.