Tsofaffi 400 sun yi maci a Uganda

Tsofaffin mata fiye da 400 ne suka yi maci a garin Entebe na kasar Uganda.

Sun yi macin ne domin nuna wa jama'a irin kalubalen da suke fuskanta.

Tsofaffin sun yi macin tare da rare wakoki inda suka shafe sa'o'i a kan titunan birnin Entebe.

Galibin tsofaffin 'yan kasar Uganda ne amma kuma wasu 'yan Kenya da Afrika ta Kudu da kuma Biritaniya sun mara musu baya.

Daya daga cikin kalubalen da tsofaffin ke fuskanta sun hada da matsalolin lura da marayun da iyayensu suka rasu sakamakon kamuwa da cutar AIDS.