Ranar kula da lafiyar ido ta duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane miliyan 240 ne ke fama da matsalar ido a duniya

Kwararrun likitocin ido na cewa dole ne mutane su lura da lafiyar idanunsu domin samun rayuwa mai inganci.

A cewar kwararrun rashin kula da lafiyar ido ka iya haifar da makanta abin da zai iya kawo wa mai nakasar ta makanta nakasu a rayuwa ta yau da kullum.

Sun kuma shawarci mutane da su guji yin amfani da magungunan da ba likitoci ne suka amince su yi amfani da su ba. Sannan kuma a guji wasa da makami da ka iya shafar lafiyar idon.

Alkaluma dai na nuni da cewa mutane kimanin miliyan 39 ne a fadin duniya ke fama da larurar makanta,a inda basa iya gani ko kadan, yayin da wasu kimanin miliyan 240 kuma ke fama da wasu larurorin na ido.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kebe ranar Alhamis ta biyu a watan Octoban kowace shekara domin zamowa 'ranar gani ta duniya' da zummar kara wayar da kan al'uma da gwamnatoci kan muhimmancin ido da kuma kula da lafiyarsa.

Taken ranar a bana shi ne, 'Kula da Ido ga Kowa'.