An samu ci gaba a harkar tsaro - Buhari

Hakkin mallakar hoto Buhari Twitter
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an samu cigaba a harkar tsaron Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya ce an samu ci gaba a harkokin tsaron kasar, wanda shi ne babban abun da ke gaban gwamnatinsa.

Buhari wanda ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin babban jami'in tsaro daga Biritaniya, ya ce ba za a samu ingantacciyar zamantakewa da tattalin arziki ba idan babu tsaro a cikin kasar.

Rikicin Boko Haram ne babban kalubale da ke gaban gwamnatin shugaba Buhari musamman a arewacin kasar, sannan kuma a kudancin kasar akwai kalubale na masu satar mutane domin kudin fansa.

A jawabinsa a ganawarsa da shugaban kasar a birnin Abuja, Babban hafsan tsaron Biritaniya, Sir Nicholas Houghton ya ce ya gamsu kwarai da gaske da irin ci gaban da Najeriya ta samu wajen yaki da ta'addaci karkashin shugabancin Muhammadu Buhari.

Janar Houghton ya tabbatarwa shugaban na Najeriya cewa Biritaniya za ta ci gaba da taimaka wa kokarin da Buhari ke yi wajen kawo karshen tayar da kayar bayan kungiyar Boko Haram.

Tun bayan da ya hau kan mulki a karshen watan Mayu, an kashe mutane fiye da 1,200 a hare-hare masu nasaba da kungiyar Boko Haram.