Nau'rar tsayar da jirgin sama mara sa matuki

Jirgin sama mara sa matuki Hakkin mallakar hoto NCSIST
Image caption Jirgin sama mara sa matuki

Wasu kamfanoni uku na kasar Biritaniya sun kirkiro na'urar hana jirgin sama marasa matuki shiga cikin wurare masu muhimmanci ta hanyar dakatar da tafiyar da yake yi a sararin samaniya.

Na'urar da aka yi wa lakabi da anti UAV tana tare sakon da jirgin marasa matuki yake aikawa zuwa inda ake sarrafa shi daga doron kasa.

Idan aka samu tangarda akwai yiwuwar cewa mai amfani da jirgin ya soma neman jirgin saboda matsalar da aka samu.

Na'urar tana cikin fasahohi na baya baya nan da za su iya harbo manyan jiragen sama marasa matuka daga sararin samaniya.

Kamfanonin sun ce nau'rar za ta iya dakatar da jirgin har na tsawon dakikoki 25.

Wani jami'i a kamfanin Enterprise Control Systems da ya kirkiro nau'rar tare da hadin gwiwar Kamfanin Blighter Surveilance systems da kuma Chess Dyanamics ya ce an yi amfani da naurar a matakin gwaji a Amurka da Biritaniya da kuma Faransa.

Mr Paul Taylor ya kara da cewa an gudanar da gwajin ne tare da hukumomin wadannan kasashe su uku.

Hukomomin kula da zirga zirgar jiragen sama sun damu a kan yadda wasu ke amfani da jirgin sama marasa matuki kusa da filin jiragen sama.

Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta Amurka, ta ce a kowane wata tana samun bayanai kusan 100 daga matukan jiragen sama da suka ce sun ga jirgin sama mara sa matuki kusa da jirginsu.