Gwamnatin Kenya na fama da talauci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya

Majalisar dokokin Kenya tana yin muhawara ta gaggawa domin binciken dalilan da suka sa gwmanatin kasar ta fada cikin talauci.

Ba a biya kudin ruwa da na wuta da na sauran abubuwan more rayuwa a kasar ba, lamarin da ya shafi akasarin ma'aikatu da hukumomin gwamnati -- har ma da ita kanta majalisar inda take fuskantar rashin wutar lantarki na tsawon kwanaki.

Dalilin haka ne ya sa hukomomin da ke kula da abubuwan da suka shafi ruwa da kuma tsaftar muhallai suka tsaya cak kuma 'yan majalisar sun ce suna cikin halin da ba za su iya jurewa ba.

Wasu daga cikinsu suna zargin baitil malin kasar da toshe hanyar samar da kudaden gwamnatin.

Faduwar darajar kudin Kenyan ta lalatawa gwamnati shirin da take yi na karbar bashi domin tallafawa kasafin kudin kasar na wannan shekarar.