Ana fargabar bullar cutar Ebola a Nigeria

Hakkin mallakar hoto

Mazauna birnin Calabar na jihar Cross Rivers da ke Najeriya sun fada cikin zulumi bayan wani mutumin da ake tsammani na dauke da cutar Ebola ya mutu.

Rahotanni sun ambato hukumar samar da agaji gaggawa ta kasar na cewa an kebe wasu mutane goma, bayan huldar da suka yi da wani mutumin da alamomin cutar suka bayyana a jikinsa.

Sun kuma ce mutumin ya rasu ne jim kadan bayan da aka kwantar da shi a asibiti.

Shugaban hukumar kula da cututtuka ta kasar, Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC cewa sai an yi gwajin jinin mutanen kafin a tabbatar ko ebola ce ta kama su.

A ranar Laraba, hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa kasashe uku da cutar ebola ta fi yi wa illa -- Guinea da Saliyo da kuma Liberia -- sun shafe mako guda na farko ba tare da samun wani da ya kamu da cutar ba tun bayan bullar cutar a shekarar 2014.