Amurka za ta sauya dabara a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan 'yan tawaye a Syria

Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta ce za ta sauya tsarin taimakon da take bai wa 'yan tawayen Syria.

Hakan ya biyo abin da ake ganin kashe makudan kudade amma kuma babu sakamako mai kyau.

A baya tsarin shi ne, Amurka ta kashe dala miliyan 500 domin taimakon mayakan 'yan tawaye su 15,000 a cikin shekaru uku.

Amma kuma a watan da ya wuce, an gano cewar mayaka dubu hudu zuwa biyar ne kawai ke fagen daga.

Pentagon ta ce a yanzu za ta bada taimakon kayayyakin soji ne kawai da kuma makamai ga kungiyoyin da suka iya kwace wasu garuruwan kungiyar IS, kamar garin Kobane da ke kan iyaka da kasar Turkiyya.

Wakilin BBC a Washington, ya ce kan Amurka ya daure, kan dabarun da za ta bullo da su a Syria saboda har yanzu ba tada karfin fada a ji kasar.