"Diezani na fama da cutar daji"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Diezani na bukatar tiyata saboda cutar daji

Tsohuwar ministar mai ta Nigeria, Misis Diezani Alison-Madueke na fama da cutar daji (cancer) kuma ta na jinya a Biritaniya.

Wata sanarwa da lauyan iyalan Madueke, Barrister Oscar Onwudiwe ya fitar, ta ce Diezani ta dade tana fama da cutar daji tun a lokacin da take ofis a matsayin minista, kuma a yanzu haka lamarin ya kara tabarbarewa.

Sanarwar ta ce tsohuwar ministar ta kamalla wani zagaye na gashin da ake yi mata na cutar daji, kuma a mako mai zuwa za a yi mata tiyata.

Lauyan ya kuma ce ta na fatan ta samu lafiya yadda zata samu damar kare kanta daga zargin da ake yi mata.

kuma musanta zargin cewar jami'an tsaro sun tsare Diezani Alison Madueke a London, inda ya ce jami'an tsaro sun gayyace ta ne kuma ta amsa gayyatar.