Blatter ya kalubalanci Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter

Sepp Blatter ya daukaka kara a kan dakatarwar da hukumar kula da kwallon kafar duniya, Fifa ta yi masa har tsawon kwanaki casa'in.

A ranar Alhamis ne Fifa ta dakatar da dan kasar Switzerland mai shekaru 79 daga aikinsa ne a kan zargin karbar hanci da rashawa.

Kazalika, Fifa ta dakatar da mataimakinsa Michel Platini da kuma Sakatare Janar na hukumar, Jerome Valcke.

Platini ma ya ce zai kalubalanci dakatar da shi din da aka yi ta hanyar da ta fi dacewa.

Tsohon shugaban kungiyoyin kwallon kafar Ingila, David Bernstein, ya gayawa BBC cewar: "Blatter ya yi rashin hankali da ya ci gaba da shugabantar hukumar na tsawon lokaci."

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika, Issa Hayatou, shi ne zai shugabanci hukumar na rikon kwarya.