An bai wa Kagame damar yin tazarce a Rwanda

Hakkin mallakar hoto
Image caption Paul Kagame dai yana mulkin Ruwanda tun 1994

Kotun kolin kasar Rwanda ta amince da sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar da za su ba wa shugaba Paul Kagame damar neman wa'adin mulkin kasar karo na uku.

Kotun kolin ta yi watsi da takardar koke da jam'iyyar Green Party ta gabatar inda take neman a hana shugaba Kagame yin tazarce.

Shi dai Shugaba Paul Kagame, wanda yake kan gaba a fagen siyasar Rwanda tun bayan kisan kare dangi na shekarar 1994, har yanzu bai fito fili ya bayyana ko zai zarce akan mulki ba, amma ana zaton yana da shirin ci gaba da kasance wa akan karagar mulki.

Wasu masana harkokin diplomasiyya dai na ganin hukuncin da kotun kasar ta yanke zai yi barazana ga dorewar dimokradiyya a nahiyar Afirka.