An hallaka mutane a Mangu da Riyom

Hakkin mallakar hoto
Image caption Bayanai sun ce jami'an tsaro sun iya yankin domin kwantar da hankali

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa an kashe mutane da dama, sannan aka kona wasu kauyuka a jerin hare-hare da aka kai a kananan hukumomin Mangu da Riyom.

Tarzomar ta barke ne a ranar Alhamis amma rahotanni na cewa yanzu kura ta lafa inda aka tura karin jami'an tsaro musamman a karamar hukumar Mangu, inda lamarin ya fi muni.

Galibin mazauna kauyukan da aka kai hare-haren dai 'yan kabilar Pyem ne da kuma Fulani.

A baya dai ana daukar karamar hukumar ta Mangu a matsayin daya daga cikin yankuna masu zaman lafiya a jihar ta Filato, amma ga alama lamarin a baya-bayana nan na neman sauyawa.

A bangare guda kuma, wasu rahotanni daga karamar hukumar Riyom na cewa akalla mutane hudu sun rasa rayukansu a wasu harin kwantan bauna da wasu 'yan bindiga suka kai a wani kauye da mazaunansa 'yan kabilar Berom ne.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ta Filato, DSP Abuh Emmanuel, ya tabbatar da kisan mutane hudu a karamar hukumar ta Riyom.

Amma ya ce kawo yanzu bai da cikakken bayani kan hare-haren da aka kai a karamar hukumar Mangu.